Daga Ibrahim Aminu Makama.
Uwar gidan Gwamnan jihar Zamfara Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana takaicin ta kan yadda ake samu Jami’an tsaro da laifin cin zarafin Mata.
Akan ta yi kira ga mahukunta da su kwarzanta duk Jami’an tsaro da aka kama da cin zarafin Mata a kafafen yada Labarai kamar yadda suke gabatar da masu laifi ga “Yan gidan Talabijin da Rediyo da Jaridu dan ya zamo izina ga sauran Jami’an tsaro.
Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana haka ne a rana ta uku na yaki da cin zarafin Mata wanda aka yi wa fyade da marasa galihu da ake tauye mahakokin su a Gusau babban birnin jihar.
Ta kara da cewa abin bacin rai shine mutane sananu ake kamawa da laifin cin zarafin Mata don haka yasa aka kaddamar da kwamitoci a kananan hukumomi don yaki da masu aikata wannan mumunan laifi dan kawo karshen su
Tace an Kuma fassara Litatafi na turancin zuwa Hausa Kan yaki da cin zarafin mata don mutane su gane illar cin zarafin Mata da kuma hukuncin da meyi zai gamu da shi.
Hajiya Huriyya ta kara da cewa, ba fyade ba ne kadai cin zarafin Mata akwai rashin kulawa ta musamman a gidajensu musamman rashin bau abinci