Daga Musa Muhammad Azare
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya yi wa majalisar zartaswarsa garambawul tare da sallamar kwamishinoni biyar nan take.
A cewar wata sanarwar da mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado,wanda ya rabawa manema labarai ,yace gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin sake farfado da harkokin mulki da kuma tabbatar da kyakkyawan fata da al’ummar jihar sukeyi gwamnatinsa.
Kwamishinonin da matakin sallamar ya shafa sun hada da kwamishiniyar ilimi, Jamila Dahiru,da kwamishinan tsaro na cikin gida , Abdulhameed Bununu,da kwamishinan yada labarai Usman Danturaki.
Sauran sun hada da kwamishinan Noma Madugu Yalams da kwamishinan kula da harkokin Addinai Yakubu Ibrahim.
Gwamna Bala ya mika godiyarsa ga kwamishinonin da ya sallama a bisa kwazo da hidima da kuma gudummawar da suka bayar wajen cigaban jihar Bauchi.
Sanarwar bata bayyana irin laifukan da kwamishinonin sukayi ba.
Gwamnan ya kuma mika sunayen mutane biyar zuwa majalisar dokokin jihar domin tantance Dan a amince masa ya maye gurbinsu da wadanda ya sallama.
A farkon watan Disamba da ya gabata na shekarar 2024 gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya dauki makamancin wanna mataki na yiwa majalisar zartaswarsa garambawul ta hanyar sallamar kwamishinoni biyar da sauyawa wasu wuraren aiki .