Manoman Najeriya sun ce za suyi biyayya ga gwamnatin tarayya a shirye shiryenta na samar da abinci da kuma rage farashin kayan abincin a Najeriya.
Manoman sunce a sakamakon kulla wata yarjijeniyar samar da abinci mai yawa ga yan kasa tsakanin asusun tallafawa manoman da Kuma Kungiyar bada horo ga manoma ta duniya an shirya kashe dala miliyan 70 domin cimma wannan bukata.
Yarjejeniyar na nufin samar da taraktocin noma guda 2,000 ga manoma gabanin daminar bana.
Yarjejeniyar ta kuma hada da kafa cibiyar samar da tsirai na da bada horon da kuma bayar da tallafin kayayyakin noma.
Har ila yau, ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya ta sanya hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar Kula da bada katin dan Kasa da nufin yiwa manoma miliyan biyu rijista a cikin watanni uku na farkon shekarar 2025 domin basu talalfi.
Shugaban kungiyar manoma ta kasa (AFAN) Alhaji Kabir Ibrahim, ya bayyana fatansa game da yuwuwar rage farashin kayan abinci domin saukakawa yan kasa.
Shugaban Kungiyar yace manoma a shirye suke su karya farashin kayan abinci tare da baiwa gwamnatin tarayya cikakken goyon baya a wannan shiri nata.