Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ci tarar Naira miliyan dubu 1 da miliyan dari 3 ga bankuna 9 saboda gazawa wajen tabbatar da samar da wadatattun kuɗade a cikin injunan cirar kudi a lokacin bikin Kirsimati da sabuwar shekara
Ko wanne banki zai biya tarar kudi naira miliyan 150 saboda rashin bin ka’idojin raba kudaden da babban bankin CBN ya yi, biyo bayan binciken da akayi a rassan bankunan a sassan Najeriya.
Sanarwar da Babban Bankin na CBN ya fitar ta tabbatar da daukar matakin, inda ya jaddada kudirinsa na samar da wadatattun kudaden takarda a hannun jama’a.
Bakunan da cin tarar ta shafa sun hada da bankin Fidelity , da First Bank da Keystone da Union Bank da bankin Globus da bankin Zenith da UBA da bankin Providus da Kuma bankin Sterling.
Babban bankin ya bayyana cewa za a cire kuɗaden tarar ne kai tsaye daga asusun bankunan da abin ya shafa.
Mukaddashin Daraktan Sadarwar Babban Bankin CBN Mrs Hakama Sidi Ali ta ce ,ba zasu zura idanu ana wahalar da yan Najeriya ba akan karancin kudade da ake kirkirar matsalar da gan gan.
Bankin na CBN yace zai Kuma binciki dalilan da suka sa suma masu Sana’ar hada hadar kudi na POS suke boye kudaden da gan gan.