Kungiyar masu noman albasa da masu dillancinta da kuma kasuwancinta a Najeriya ta ce ambaliyar ruwa da kuma karancinta sune dalilan da suka janyo albasar ke tsada a sassan kasar nan.
Shugaban kungiyar mamonan Albasa na Najeriya Aliyu Isah ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Legas.
Rahotanni nacewa an fuskanci tashin gwauron zabi na Albasa a Najeriya tun daga watanni ukun Karshen shekarar 2024 har zuwa yanzu inda ake sayar da buhu tsakanin N250,000 zuwa N270,000 sabanin N70,000 da N90,000 kan kowanne buhu a watannin baya.
Shugaban Kungiyar masu noman albasar yace ,ambaliyar ruwa na daga cikin abinda ya haddasa karancin albasar a Najeriya.
Ambaliyar ruwan da aka fuskanta a jihohin Arewa a 2024 wacce ta mamaye gonakin albasar sun hada da jihohin Sokoto da ,Kebbi,da Zamfara,da Kano, da Kaduna,da Katsina, da kuma Adamawa.
A Sokoto ambaliyar ruwan da aka samu a sassan jihar a sakamakon ballewar madatsar ruwa ta Goroyo, ya shafi gonakan albasa da dama ,Kuma hakan yasa anyi hasara da yawa.
Saidai Kungiyar na fatan hada kai da gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa dan kawo sauki ga al’ummar Najeriya.