Rahotanni nacewa akwai yiwuwar kamfanoni sadarwa za su ƙara kuɗin kira da na data da kuma tura rubutaccen saƙo a farkon sabuwar shekarar 2025.
Wani babban jami’in daya daga cikin kamfanin sadarwa na Najeriya shine ya sanar da hakan.
Rahotanni nacewa kamfanonin suna da ƙwarin gwiwar samun sahalewar Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) domin kara kuɗin kira da na data da tura takaitaccen sakon karta kwana.
Jami’in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa kamfanonin sadarwar na MTN da Airtel da 9Mobile sun riga sun aika wa hukumar NCC buƙatarsu na yin karin kuma bisa dukkan alamu suna ganin hukumar zata mika wuya.
Idan za’a iya tunawa hukumar ta NCC ta ƙi amince wa kamfanonin ƙara kuɗin kiran waya da Data tun a zamanin tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami kuma har ya sauka daga kujerar ba’a karawa yan Najeriya ba.
Kimanin shekara 10 ke nan kamfanonin suke neman ƙara kuɗaden saboda abinda suka dogara dashi na hauhawar farashin kayayyaki, amma gwamnati tana ƙin ba su damar yin hakan.