Hukumar ‘kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje tace a yanzu haka akwai mata sama da 5000 da suka makale a Kasar Iraqi kuma yawancinsu matan Aure.
Hukumar tace matan na fuskantar cin zarafi da muzgunawa da sauran sun.
Shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa ta ce matan sun yi balaguro ne zuwa Iraki a karan kansu wasu kuma mazansu ne suka tura su domin yin aikatau ko yiwa yan kasar hidima da sauran abubuwan da suka shafi bautarwa,sai kuma a yanzu haka matan sun makale acan.
Ta bayyana hakan ne a Legas a yayinda take jawabi ga mahalarta taron karawa juna sani kan “Shirin wayar da kan jama’a don inganta hanyoyin zuba jari a yankin Kudu-maso-Yamma.
Duk dacewa hukumar bata fadi daga shiyar da matan sukafi fitowa ba,Amma wata majiya ta shaida cewa matan auren sunfi yawa daga shiyar Arewa maso yamma da arewa maso gabas.
Rahotanni nacewa da yawa daga cikin ‘yan Najeriya musamman mata sun makale a kasashen waje bayan sun yi tafiya ta hanyoyin da ba su dace ba domin aikatau acan.
Dabiri-Erewa ta shaida wa mahalarta taron da aka zabo daga jihohin Kudu-maso-Yamma cewa, akwai dimbin damarmaki a Najeriya maimakon yin hijira da sunan neman aiki mai tsoka wanda a karshe mutum zai sha wahala koma a rasa rai a Inda ya je.
Shugabar ta bada misali da yadda magidanci ya tura matarsa zuwa kasar Iraqi domin ta zama mai hidima ga wasu amma matar ta mutu saboda zargin cusguna mata da akayi ,kuma yanzu haka Ofishin Jakadancin Najeriya na taimakawa wajen dawo da gawarta gida.
Tace a yanzu haka data bincika akwai mata sama da 5000 da suka makale a Iraqi ana azaftar dasu Kuma yawancinsu matan Aure ne.
Ta kara dacewa yanzu babban kalubalen da suke fuskanta shine kokarin dawo da matar auren da ta mutu a Kasar Iraqin.
Ta gargadi magidantan Najeriya da su guji tura matansu zuwa kasashen waje aikatau .