Rahotanni daga garin Bida a jihar Naija na cewa matasa maza da mata sun sake mamaye wata motar tankin mai  da ta fadi domin kwasar man dake malala a kasa.

Wannan na zuwa ne  Kwanaki biyu bayan da wasu mutane yawancinsu matasa suka kone kurmus wasu kuma suka jikkata sakamakon faduwar wata tankar man fetur da ta fadi a jihar Neja, Kuma ta kama da wuta bayan fara kwasar man dake zuba a kasa , a garin Dikko na jihar Naija a ranar Asabar.

Sai dai wata mazauniyar garin Bida a jihar Naija Fatimah Muhammad,ta shaidawa Jaridar PREMIUM TIMES cewa tankar na dauke ne da man gyada ba fetur ba.

Rahotanni nacewa faduwar babbar motar dakon man gyadar keda wuya sai mata da Maza da harda matan aure sukaita fitowa suna kwasar man.

Anga yadda jami’an tsaro suke ta korar mutane,Amma hakan bai hana mutane cigaba da kwasar man gyadar suna guduwa dashi ba.

Motar wacce ta fadi a kusa da gidan man fetur na AYM Shaffa dake garin Bida anga yadda mutane suke ta dibar man na gyada a mazubai,ciki harda kwanukan girki da tukwane .

TST Hausa ta rawaito cewa duk da babu wata fargaba sosai na fashewar tankar dakon man gyadar,Amma hakan na faruwa ne kwana biyu bayan mutane 100 sun mutu sama da 60 sun jikkata a lokacin da wuta ta tashi jim kadan da fara kwasar man fetur din wata tirela ta dakon fetur a mahadar Dikko dake jihar Naija.

Haka Kuma ko a watan Oktoban bara saida mutan 170 suka rasa rayukansu a garin Majiya dake karamar hukumar Taura ,bayan fashewar tankar dakon man fetur da ta kama da wuta ,wacce itama aka fara kwasar man fetur din da take dauke dashi bayan ta fadi.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version