Al’umar garin Ugama dake karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna sun shiga furgici bayan da wasu mutane da ake zargin yan banga ko yan kato da gora suka kutsa kai cikin garin na Ugama Inda suka rika yiwa mutane yankan Rago tare da sace dukiyoyinsu.

TST Hausa ta rawaito cewa mutanan garin wadanda Fulani ne a yanzu haka sun tsare daga garin ciki harda mata da kananan yara.

Shaidun gani da Ido sun shaida cewa a kalla mutane 20 akayiwa yankan rago,sannan an jikkata wasu da  dama.

Acewar wani magidanci Malam Yusufa Ugama wanda ya tsira da ransa kuma ya zanta da TST Hausa yace bayan yiwa mutane yankan rago, mutanan sun kuma cinnawa garin nasu wuta.

Sannan Kuma mutanan da ake zargi yan Kato da gora ne sun sace dabbobinsu.

Har yanzu ba’a san dalilin kai harin ba .

“Kaiwa sai muka ga mutanan dauke da bindigogi da gorori da wukake ,Kuma suna  kiran kansu a matsayin yan kato da gora”Acewar Yusufa

Wata majiya ta shaida cewa ,an jima ana takaddama tsakanin mutanan garin da Kuma dagacinsu wanda ba’a ambaci sunansa ba akan batun neman sayar da gonakan nasu.

A yayinda TST Hausa ta tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna DSP Mansur Hassan ya tabbatar da faruwar lamarin.

Saidai yace har yanzu rundunar bata samu wani korafi daga mutanan garin ba ,ko wata Kungiya kan batun da kuma wadanda ake zargi da kisan kiyashi.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version