Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kutsa kai cikin babban asibitin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda suka harbe wani likita ya mutu nan take tare da yin garkuwa da wasu ma’aikatan asibitin mutane biyar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina DSP Abubakar Aliyu ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Aliyu ya bayyana cewa wadanda suka jikkata na samun kulawa likitoci yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da zakulo masu laifin domin kama su.
Yace suna iya kokarinsu domin kubutar da ma’aikatan lafiyar da aka sace a Asibitin.
Ya kara da cewa a halin yanzu ana gudanar da bincike kan lamarin.
A cewarsa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Abubakar Musa, yayi Allah wadai da harin.
Ya kuma jajantawa iyalan likitan da ya mutu da wadanda duka jikkata.