Shugaban Kungiyar rundunar yan kishin Kano Manjor Janar Ibrahim Sani Yakasai mai ritaya ya kaddamar da wani kwamatin tsaro na musamman da zai sasanta fadace fadacen Daba da kwacen waya a birnin Kano da kewaye.

Manjor Janar Ibrahim Yakasai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa.

Yace an kaddamar da kwamatin ne karkashin jagorancin Kungiyarsa ta rundunar kishin Kano bayan,sun fahimci cewa yan dabar da ake zargi da hana Kano zama lafiya da kuma kwacen waya a shirye suke su mika wuya domin samun zaman lafiya a Kano.

Yace kwamatin tsaro  na  gano  matasan masu fadace fadacen Daba a kano ya kunshi masu unguwanni da yan kwamatin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a unguwanni.

Manjo Janar Ibrahim Yakasai mai ritaya ya lissafo wasu unguwanni a birnin Kano guda 8 da zasu fara zakulo matasa masu fadan Daba da kwacen Waya,Inda yace anan matsalar tafi kamari a birnin Kano.

Unguwannin sun hada da Yakasai A da B da Durumin Zungura da Zage da Zango da Soron Dinki da Unguwar Fagge da Kofar Nasarawa da Kuma unguwar Satatima .

Yakasai cikin yanayi na damuwa yace a matakin farko suna lallaba matasan da rarrashinsu kan su mika wuya,Amma idan suka Kaisu bango zasuyi amfani da karfin tuwo wajen murkushesu .

TST Hausa ta rawaito cewa an zabi Muayyad Malam Hadi daga unguwar Fagge a matsayin Shugaban kwamatin hadin guiwar da zaiyi wannan aiki ,sai Kuma Nasiru Uba daga Yakasai B a matsayin Mataimakin Shugaba

Sauran Yan kwamatin sun hada da Bello Adamu daga Unguwar Yakasai A a matsayin Sakatare,da Umar Haruna daga Kofar Mata a matsayin Ma’ajin Kudi.

Sai Kuma Fatihu Isa Abdullahi daga Zango da Zage a matsayin jami’in tsare tsare da Abdullahi Alo Alo daga unguwar kofar Nasarawa a matsayin mai tsawatarwa da Kuma Garba Usaini Danmaliyo daga Durumin Zungura a matsayin mai duba yiyuwa samar da aikinyi ga matasan .

Anan gaba ake sa ran samar da rana ta musamman da za’a zauna da Yan Dabar a birnin Kano a wani kebabban waje

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version