Tsohon kwamishinan raya karkara na jihar Kano Abbas Sani Abbas ya fice daga jam’iyar NNPP kwankwansiyya mai mulkin Kano zuwa jam’iyar APC mai mulkin kasa.
Abbas Sani Abbas Wanda gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga mukamin kwamishinan raya karkara ya koma APC tsagin Mataimakin Shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibiril.
A cikin wani faifan Bidiyo da aka turawa TST Hausa domin tantance ainin abinda ya faru anga yadda Sanata Barau Jibiril ya cirewa Sani Abbas jar hula ya dora masa wata daban ,inda Shugaban Abdullahi Abbas ya kasance a wajen
A ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2024 ne gwamna Yusuf na jihar Kano yayi garambawul a majalisar zartaswarsa ciki harda sauke kwamishinoninsa guda biyar,wanda Abbas Sani Abbas Yana daga ciki.
TST Hausa ta rawaito cewa daga wannan lokaci ne Abbas Sani Abbas ya rika shiga kafafen yada Labarai yana suka ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
A yayinda yake jawabi bayan fita daga tafiyar Kwankwasiyya, Abbas Sani Abbas yace zaici gaba da hada kai da gwamnatin APC bangaren Barau domin ciyar da jam’iyar gaba.
Abbas Sani Abbas yace ya bar tafiyar Kwankwasiyya ne saboda rashin adalci, musamman a gareshi da kuma wadanda suka taho tare.
Ana sa ran nan gaba , tsohon kwamishinan zai kai ziyara wajen Shugaban jam’iyar APC na kasa.