Daga Sani Dan Bala Gwarzo
Tsohuwar gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana gwamnatin kwankwansiyya karkashin jagoranci gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wacce bata tabuka abin azo a gani ba a jihar Kano.
Tsohon kwamishinan kasafin kudi da tsare tsare na jahar kano,Alh Ibrahim Dan Azumi Gwarzo ne ya bayyana hakan a yayin ganawar sa da manema labaarai a birnin Kano.
Tsohon kwamishinan wanda yake takarar Shugabancin jam’iyar APC a Kano yace gwamnatin jahar kano babu abinda ta yi al’ummar Kano a zahiri da za’ayi alfahari dashi.
Gwarzo yace abubuwan da jam’iyar APC tayi a Kano za’a jima ba’a manta dasu ba.
Ya jaddada cewa a shirye APCn take ta karbe mulki a hannun NNPP a zaben 2027 a Kano.
Ya nemi ‘ya’yan jam’iyar APC na Kano da suci gaba da hada kansu dan samun nasarar jam’iyar a zaben 2027 mai zuwa .
Dan Azumi Gwarzo yayi alkawarin hada kai da dukannin masu ruwa da tsaki tare da shugabanin APC a kananan hukumomin Kano,idan ya samu nasara wajen ciyar da jam’iyar gaba