Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Alhaji Shehu Musa Gabam ya tabbatar dacewa, Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ba zai taba kai labari ba a zaben shekarar 2027.

Shehu Gabam ya bayyana wasu daga cikin dalilin da ya sa Bola Tinubu ba zai sake lashe zaben 2027 ba.

Gabam ya ce yawanci shuwagabannin da suka gabata a Najeriya da suka haifar da matsaloli a Najeriya musamman rusa tattalin arzikin Kasar da haifar da matsalar tsaro a cikin shekaru biyun farko na wa’adin mulkinsu ba su taba lashe zaben wa’adi na biyu ba.

Yayi wannan magana ne yayin da ake tattaunawa dashi a shirin Siyasa a yau na gidan talabijin din Channels a Abuja.

Gabam ya tunatar da Yan Najeriya cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sha Kaye ne saboda yadda aka fara adawa da gwamnatinsa a shekaru biyun farkon wa’adin mulkinsa na farko.

Ya nemi yan Najeriya su hada kansu domin ceto Najeriya daga halin kunci da karayar tattalin arziki da Gwamnatin Bola Tinubu ta jefa ta a ciki.

Shugaban jam’iyar ta SDP Shehu Musa Gabam,na wannan jawabi ne kasa da awanni 24 bayan da shi kuma Tsohon dan majalisar dattawa daga Kaduna ta tsakkiya Sanata Shehu Sani ya shaida cewa yan Arewa basu da hujjar kin sake zaban Tinubu a shekarar 2027.

Haka Kuma yace ko kalubalantar Tinubu bai kamata yan Arewa suyi ba,saboda sunga yadda tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lalata kasar nan,Amma aka rasa masu fada masa gaskiya ko kalubalantarsa a wancan lokacin.

Saidai TST Hausa ta gano cewa da yawa daga cikin yan arewancin Najeriya na caccakar Shehu Sani din saboda kalaman nasa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version