Gwamnatin Tarayya ta sanar da Talata, 25 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin murnar ranar Haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ce ta sanar da hakan, inda ta bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki matakin ne domin bai wa Musulmi damar gudanar da bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Gwamnatin ta taya al’ummar Musulmi murnar wannan muhimmiyar rana, tare da yin kira gare su da su yi amfani da bikin wajen yin tunani kan koyarwar Annabi Muhammad (SAW), musamman zaman lafiya, haƙuri, tausayi, yafiya da taimakon juna.

Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya baki ɗaya da su ci gaba da gudanar da bukukuwan cikin lumana, tare da ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Bisa wannan sanarwa, Talata, 25 ga Agusta, za ta kasance ranar hutun jama’a, yayin da ma’aikata za su koma bakin aiki bayan kammala hutun.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version