Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar, inda ya doke ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, da tazarar kuri’u 66,252.
Sakamakon zaben da aka kammala tattarawa daga kananan hukumomi 30 na jihar ya nuna cewa Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya samu kuri’u 511,067, yayin da babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC, ya samu 444,815.
Ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri’u 17,180.
Nasarar ta bai wa Adeleke damar ci gaba da mulkin Jihar Osun a wa’adinsa na biyu, bayan ya sake samun rinjaye a sassa daban-daban na jihar.
Sakamakon da aka tattara ya nuna cewa Adeleke ya samu gagarumar nasara a wasu daga cikin manyan kananan hukumomin jihar, ciki har da Ede North, Ede South, Osogbo, Ife East, Ife Central, Iwo, Egbedore da Oriade.
A Osogbo, Adeleke ya samu kuri’u 36,480, yayin da Oyebamiji ya samu 30,474. A Ede North kuma, Adeleke ya samu 35,427, yayin da abokin hamayyarsa ya samu 10,283.
Sai dai jam’iyyar APC ta samu nasara a wasu muhimman kananan hukumomi, ciki har da Irewole, Boripe, Ilesa East, Irepodun, Obokun, Atakunmosa West da Olorunda.
A Irewole, Oyebamiji ya samu 29,972 yayin da Adeleke ya samu 10,934, yayin da a Boripe APC ta samu 19,963 kan 12,448 da Accord ta samu.
Duk da tsananin fafatawar da aka samu tsakanin jam’iyyun biyu, sakamakon karshe ya nuna Adeleke a kan gaba da tazarar 66,252.
Hakan ya tabbatar da nasarar Adeleke wajen neman wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan Jihar Osun, bayan ya samu rinjaye a zaben da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta, 2026.
