Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta gudanar da wani shirin wayar da kan jama’a kan muhimmancin kalandar Musulunci (Hijri) da rawar da take takawa wajen gudanar da ibadu da sauran muhimman al’amuran rayuwar Musulmi.

Gwamnatin Jihar Kano ce ta dauki nauyin shirin, wanda aka gudanar da shi da nufin kara fahimtar al’umma game da kalandar Hijri, tarihin samuwarta da kuma muhimmancin sanin watanni da ranakun Musulunci.

Kwamishinan na Biyu na Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, Sheikh Ali DanAbba, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan manufar shirin.

Sheikh Ali DanAbba ya bayyana cewa kalandar Musulunci ba kawai wata hanya ce ta kirga kwanaki ba, illa tana da muhimmiyar rawa wajen tsara da gudanar da manyan ibadu da bukukuwan Musulunci.

Ya ce sanin watanni da ranakun Hijri na da matukar muhimmanci, musamman ganin cewa ibadu kamar azumin Ramadan, Hajji da bukukuwan Idi, da sauran muhimman lokutan ibada, suna da alaka kai tsaye da kalandar Musulunci.

Kwamishinan ya kara da cewa matakin Gwamnatin Jihar Kano na daukar nauyin samar da kalandar Musulunci ya nuna muhimmancin da take bai wa harkokin addini, tare da kokarin tabbatar da cewa al’umma na samun sahihin bayani kan muhimman ranakun kalandar Hijri.

A yayin taron, Malam Ibrahim Falaki, wanda ya gabatar da takarda kan wannan batu, ya yi bayani kan tarihin kalandar Musulunci, asalin samuwarta da kuma muhimmancin da take da shi ga Musulmi.

Ya bayyana cewa fahimtar kalandar Hijri na taimaka wa Musulmi wajen gudanar da wajibai na addini yadda ya kamata, tare da fahimtar muhimman abubuwan tarihi da suka shafi addinin Musulunci.

Malam Ibrahim Falaki ya yi kira ga Musulmi da su kara bai wa kalandar Hijri muhimmanci tare da amfani da ita wajen tsara muhimman al’amuran rayuwarsu, musamman wadanda suka shafi ibada.

Ya kuma jaddada bukatar ilmantar da matasa da sauran jama’a kan kalandar Musulunci, domin kare ilimin addini da kuma kara fahimtar tarihin da koyarwar Musulunci.

Taron ya samu halartar malaman addini, jami’an Hukumar Shari’a da sauran masu ruwa da tsaki, inda aka jaddada bukatar ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin kalandar Musulunci da yadda ya kamata a yi amfani da ita.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version