Shugaban Asibitin Kwararru na Best Choice da ke Kano, Auwal Lawal Muhammad (Dan Malikin Garo), ya taya Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da al’ummar jihar Kano, da ma daukacin Musulmin duniya murnar zagayowar Maulidin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama.

A cikin sakon taya murnar, Auwal Lawal ya yaba wa Gwamnan Kano kan kokarinsa na hada kan al’ummar jihar, musamman a harkokin addini, domin magance rarrabuwar kawuna da karfafa fahimtar juna tsakanin al’umma.

Ya bayyana cewa irin wannan lokaci na Maulidi wata dama ce ga al’umma da su kara kusantar Allah, tare da yawaita addu’o’in neman zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban kasa baki daya, musamman jihar Kano.

Shugaban Asibitin Best Choice ya kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kokarin da yake yi wajen inganta fannin kiwon lafiya a jihar.

Ya ce gwamnatin jihar na daukar matakai wajen gyara da inganta asibitoci, samar da kayayyakin aikin likitanci na zamani, tare da horas da ma’aikatan lafiya domin inganta ayyukan kiwon lafiya da kuma saukaka wa al’umma samun ingantaccen magani.

A karshe, Auwal Lawal Muhammad ya yaba wa Gwamnan bisa sadaukarwarsa da kuma tausayi da yake nunawa ga al’umma, yana mai cewa irin wadannan halaye na shugabanci suna da matukar tasiri wajen inganta rayuwar jama’a da ci gaban jihar Kano.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kara bai wa Gwamnan lafiya da basira wajen gudanar da mulkin jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a Kano da Najeriya baki daya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version