Fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa tun bayan da aka fara kafa gwamnatoci a Jihar Kano, ba a taɓa samun gwamna mai haƙuri da juriya irin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.
Rarara ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, yayin ziyarar da ƙungiyar Triple R ta kai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na da halin haƙuri da juriya, wanda a cewarsa, hakan ya sa ya bambanta da gwamnonin da suka gabace shi wajen tafiyar da mulkin jihar.
Rarara ya kuma yaba wa gwamnan kan yadda yake gudanar da harkokin mulki, yana mai cewa haƙuri na daga cikin muhimman halayen da ake buƙata wajen jagorantar al’umma.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa mambobin ƙungiyar Triple R bisa jajircewarsu wajen wayar da kan al’umma da kuma ƙoƙarin ganin an sake zaɓar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da sauran gwamnoni a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027, ciki har da shi kansa.
Gwamna Yusuf ya kuma yi alƙawarin tallafa wa ƙungiyar Triple R wajen gudanar da ayyukanta, tare da samar musu da abubuwan da suke buƙata domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Gwamnan ya kuma nuna gamsuwa da ziyarar yan kungiyar ta Triple R tare da nuni da irin kishin da Shigaban Kasa Bola Ahamad Tinubu ke da shi da kuma cigaban da ya kawo Arewa.
Ya kuma shaida cewa da ana samun matasa irin yan Triple R suna yada nasarorin da Bola Tinubu ke kawowa Arewa to da Tinubu baiyi yakin neman sake zabensa ba.
