Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Borno, Saina Buba, ya janye kalaman da ya yi a baya da suka haifar da ce-ce-ku-ce, tare da neman afuwar al’ummar jihar da sauran jama’a.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a Maiduguri ranar Laraba, Buba ya ce kalaman nasa ba su da nufin cutar da kowa ko tauye wa jama’a ’yancin zaɓe da ’yancin shiga kowace jam’iyyar siyasa da suke so.

Kwamishinan ya ce furucin da ya yi a wani shirin ƙarfafa gwiwar matasa da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya a Maiduguri ya jawo damuwa a tsakanin jama’a.

Ya bayyana cewa, duk da cewa a baya ya yi ƙarin bayani cewa ba a yi furucin ne da ma’anarsa ta zahiri ba, ya yanke shawarar janye kalaman nasa a hukumance tare da ba al’ummar Jihar Borno da sauran jama’a haƙuri bisa damuwar da suka haifar.

Buba ya kuma bayyana cewa kalaman nasa ba sa wakiltar manufofin jam’iyyar APC ko gwamnatin Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.

Ya ce gwamnatin Zulum da jam’iyyar APC suna mutunta ’yancin jama’a tare da kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa na zaɓe da kuma shiga ƙungiyar siyasar da yake so.

Furucin kwamishinan ya jawo ce-ce-ku-ce a kwanakin baya, musamman bayan ya yi barazanar cewa za a karya yatsun waɗanda suka nuna adawa, lamarin da ya sa aka samu kiraye-kirayen a binciki kalaman nasa.

Rahotanni sun ce ’yan sanda ma sun fara bincike kan zargin kalaman tayar da hankali da suka shafi wasu ’yan siyasa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version