Daga Ibrahim Aminu Makama

Dahir Abdulrahim, wani masani kan sha’anin wanzar da zaman lafiya kuma shugaban Gidauniyar Darul Al-khair Foundation, ya bayyana cewa rashin isasshen kulawa ga kananun jami’an tsaro na daga cikin manyan dalilan da ke kawo matsalar tsaro a Najeriya. 

A wata hira da ya yi da jaridar TST media  Dahir ya nuna damuwarsa game da yadda rashin kulawa ga sojoji da ƴan sanda ke kara haifar da tabarbarewar sha’anin tsaro. Ya yi kira ga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da ya duba lamarin, tare da yin aiki don inganta jin dadin kananun jami’an tsaro ta hanyar: 

Kara albashi da kyautata yanayin aiki: Wannan zai taimaka wajen kara musu kwarin gwiwa wajen aiwatar da ayyukansu. 

Bada horo na musamman: Horo da kayan aiki na zamani suna da mahimmanci wajen tabbatar da kwazon jami’an tsaro. 

Tallafawa da walwala: Samar da tallafin gidaje, lafiya, da tsaro na iyalai zai kara musu kwarin gwiwa. 

Dahir Abdulrahim ya kuma yaba da kokarin gwamnati na kawo sauyi a sha’anin tsaro, amma ya jaddada cewa dole ne a bai wa kananun jami’an tsaro muhimmanci fiye da yanzu. 

Ya yi kira da cewa idan ba a dauki mataki ba, tabarbarewar tsaro ka iya kara kazancewa, wanda zai shafi tattalin arzikin kasa da zaman lafiyar al’umma gaba daya. 

Gidauniyar Darul Al-khair Foundation tana daga cikin kungiyoyin da ke taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa marasa galihu da kuma wanzar da zaman lafiya a Najeriya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version