Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada ƙudirin ta na yaƙi da rashin aikin yi,da rage talauci da kuma kawo ƙarshen matsalar bara ta hanyar zuba jari a fannin koyar da sana’o’in hannu da fasaha.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar kula da Kere-kere da Kayayyakin Kimiyya da Injiniya ta Ƙasa (NASENI) ta ƙaddamar da wani gagarumin shirin horaswa da ƙarfafa tattalin arziƙin mata da matasa a Jihar Kano.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, wakilin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, Musaddiq Mustafa Adamu, ya yaba wa NASENI bisa irin gudunmawar da take bayarwa wajen cika manufofin Gwamnatin Tarayya na bunƙasa tattalin arziki ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha da koyar da sana’o’i.

Ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da damar da suka samu wajen gina rayuwarsu, su dogara da kansu tare da zama masu samar wa wasu ayyukan yi a nan gaba.

A nasa jawabin, Kwamishinan Kuɗi na Jihar Kano, Ismail Aliyu Dan Maraya, wanda ya wakilci gwamnatin jihar, ya bayyana shirin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci.

Yace shirin zai kuma,taimaka matuƙa wajen rage zaman banza da bunƙasa tattalin arzikin al’umma.

Ya ce Jihar Kano ta yi farin cikin kasancewa cikin jihohin da suka amfana da wannan shiri, tare da bayyana cewa ilimi da ƙwarewar da mahalarta suka samu za su ba su damar kafa sana’o’i, samar da kuɗaɗen shiga da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin jihar.

Tun da farko, Shugaban Hukumar NASENI kuma Babban Darakta, Khalil Suleiman Halilu, ya ce haɗin gwiwar da hukumar ta yi da Gwamnatin Jihar Kano na horas da mata da matasa kan sabbin fasahohi zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage talauci da kuma magance matsalar bara.

Ya bayyana cewa shirin an tsara shi ne domin bai wa matasa ƙwarewar aiki da za ta sa su dogara da kansu, tare da ba su ilimin girkawa da kula da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana (Solar), wanda zai taimaka wajen magance matsalolin wutar lantarki a al’ummomi.

Ita ma Shugabar Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u, ta buƙaci a faɗaɗa irin wannan shiri zuwa yankunan karkara, tana mai cewa matasa da dama a ƙauyuka na da hazaka da basirar da za su iya amfani da ita wajen inganta rayuwarsu idan aka ba su irin wannan damar koyon sana’a da samun tallafi.

Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin sun bayyana cewa horaswar da suka samu da kuma kayan aikin fara sana’a da aka ba su sun sauya musu tunanin rayuwa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version