Hukumar Bunƙasa Kimiyya da Kere-kere ta Ƙasa (NASENI) ta ƙaddamar da wani shiri na musamman domin ƙarfafawa mata guiwa ta hanyar koyar da su sana’o’in fasaha da za su taimaka musu su dogara da kansu tare da taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki.

Da yake jawabi a Kano yayin ƙaddamar da shirin, Shugaban NASENI, Alhaji Khalil Sulaiman Halilu, ya ce an tsara shirin ne domin horas da mata kan haɗawa, girkawa, gyarawa da kula da na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana (Solar), domin su samu damar dogaro da kansu ta hanyar sana’a.

Mata 50 daga ƙananan hukumomin Kumbotso da Tarauni ne suka amfana da horon na kwanaki uku, wanda shi ne matakin farko na shirin da ake sa ran za a faɗaɗa zuwa dukkan ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Alhaji Halilu ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin mata tare da ba su damar samun hanyoyin shiga na halal.

Ya ƙara da cewa akwai buƙatar ƙara yawan mata masu aikin gyaran na’urorin hasken rana, musamman a Arewacin Najeriya inda wasu al’adun gargajiya kan sanya wahala ga maza shiga wasu sassan gidaje domin gudanar da irin waɗannan ayyuka.

A cewarsa, duk da cewa an fara shirin ne a Kano, an tsara shi ne domin aiwatarwa a faɗin ƙasar nan, a matsayin wani ɓangare na manufofin NASENI na bunƙasa fasaha da ƙarfafa mata.

Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa NASENI ta riga ta horas da dubban mata a fannoni daban-daban da suka haɗa da gyaran taraktoci, fasahar jiragen sama marasa matuƙi (drones) da sauran sana’o’in kere-kere.

Wasu daga cikin mahalartan horon sun bayyana farin cikinsu da wannan dama da suka samu, suna masu cewa ilimin da suka samu zai taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da kuma taimakawa al’ummominsu.

A nata jawabin, Injiniya Khadijah Garo, wadda ta wakilci Mai Bai Wa Gwamnan Kano Shawara Kan Ilimin Mata, ta ce shirin ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Jihar Kano na ƙarfafa mata ta hanyar ilimi da koyon sana’o’i domin su zama masu dogaro da kansu.

Ta yabawa NASENI bisa kawo wannan shiri zuwa Kano tare da nuna godiya ga irin gudunmawar da hukumar ke bayarwa wajen inganta rayuwar mata da sauran al’ummar jihar.

Domin tabbatar da cewa mahalartan za su fara aiki nan take bayan horon, an ba su takardun shaidar kammala horo tare da kayan aikin sana’a, domin su fara gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ba.

NASENI ta ce wannan shiri wani ɓangare ne na ƙudirin ta na haɓaka kirkire-kirkire, bunƙasa sana’o’i da kuma ƙara yawan mata masu shiga harkokin kimiyya da fasaha a Najeriya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version