Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya bayyana cewa za a ɗauki tsakanin kwanaki uku zuwa huɗu kacal domin kammala jigilar Alhazan jihar Kano zuwa gida da zarar an fara aikin kwaso su daga ƙasar Saudiyya.
Ya bada tabbacin cewa za’a fara mayar da Alhazan Kano ne a ranar 24 ga watan Yuni na 2026.
Matawalle ya bayyana hakan ne a birnin Makka yayin wani taro da jami’an kula da Alhazan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, inda ya yi bayani kan shirye-shiryen da aka yi domin tabbatar da cewa komawar Alhazan gida ta gudana cikin tsari da nasara.
Ya ce hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace domin sauƙaƙa wa Alhazan tafiyar komawa gida bayan kammala ibadun Hajjin bana.
Shugaban hukumar ya tabbatar wa Alhazan da iyalansu cewa babu wani shiri na sake sauya jadawalin tashin jirgin Alhazan na Kano Kamar yadda aka da tsara, yana mai jaddada cewa komai yana tafiya yadda aka tsara.
Ya kuma yi kira ga Alhazan da su ci gaba da ba jami’an hukumar haɗin kai tare da bin umarnin da ake ba su domin tabbatar da cewa aikin jigilar su zuwa gida ya gudana cikin kwanciyar hankali da nasara.
Matawalle ya yabawa jami’an hukumar da sauran masu ruwa da tsaki bisa ƙoƙarin da suke yi wajen kula da Alhazan jihar Kano tun daga farkon aikin Hajji har zuwa wannan lokaci na komawa gida.
