Jami’ar PDP ta rarrashi tsohon Shugaban kasa Good luck Jonathan da ya sake tsaya mata takarar Shugabancin Najeriya a shekarar 2027.

Mataimakin Sakataren yada yada labarai na jami’yar PDP Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana bukatar hakan a hirarsa da manema labarai.

Yace PDP a yanzu bata da wani dan takara mai farin jini da gogewa a siyasa wanda Kuma Yan Najeriya ke kewarsa sama da Jonathan.

Ya ce idan aka duba irin gogewarsa da hakurinsa da kokarin ciyar da Najeriya gaba ,shi ya kamata ya tsayawa jami’yar takara (JONATHAN)

PDPn tace ko Ministan Abuja aka duba irin gudun mowar da yake bayarwa wanda dan PDP ne ansan jami’yar ta kama hanyar karbar Mulki a 2027.

Da aka tambayeshi ko hakan na nufin zasu ajiye Atiku su dauki Jonathan anan sai baiyi Karin bayani ba Inda yace Demokaradiyya akeyi a Najeriya.

A kwanan nan anga yadda hotunan tsayawa takarar Shugabancin Najeriya na Good luck Jonathan ke ta yawo a birnin Kano Wanda ya dauki hankalin jama’a.

PDP tace babbar hasara ce Jonathan din yaki karbar wannan tayi nata.

Jonathan ya fadi zabe ne a shekarar 2015 Kuma tun daga nan ba’a taba ji daga bakinsa ya sake neman takarar Shugabancin Najeriya ba .

Ko yanzu da PDP ke zawarcinsa , ba’a ji tabakinsa ba tukunna .

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version