Tsohon Shugaban hukumar kula da makarantun sakandare ta Jihar Kano (KSSSMB), gidan Malamai Dokta Bello Shehu, ya taya tsohon gwamnan kano kuma Shugaban jami’yar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje bikin cika shekara 75 da haihuwa a duniya

A cikin wata sanarwa da Dr.  Shehu ya sanyawa hannu ya bayyana Ganduje a matsayin dattijon arziki,mai hangen nesa ,shugaba abin koyi ,mai tausayawa jama’arsa, jagora na gari,Kuma abin koyi a siyasar Arewa dama Najeriya baki daya.

Yace mai girma jagora ,a matsayinka na tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma a yanzu a matsayinka na Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, hakika kabar tarihi a siyasar Najeriya.

Ya ce idan aka duba  irin gudunmawar da Dr. Ganduje ya bayar a fannin ilimi, kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa, babu shakka sai anyi da gaske za’a kamo shi a kano wanda yace  jajircewarsa ce tasa ya kawo wannan matsayin a Najeriya.

Da yake yin tsokaci game da mulkinsa a Kano ,Dr Shehu ya bayyana mulkin Dakta Ganduje, a matsayin wani babban gibi da ya bari a siyasar kano wajen cigaban ilimi da za’a jima ba a mayar ba mutukar ba’a tashi tsaye ba .

Dokta Shehu ya yi addu’ar Allah ya kara wa Dakta Ganduje nasara da lafiya, inda ya ce, hikimarsa , da tawali’u, da ya nuna a mulkinsa na cigaba da zama abin koyi.

A watan Yulin shekarar 2019 tsohon gwamnan na kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada Dr Bello Shehu a matsayin Shugaban hukumar kula da makarantun sakandare ta kano,wanda tun bayan barinsa wajen , ma’aikata da dama suke kewarsa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version