Babban Limamin Masallacin Juma’a na Usman Bin Affan da ke Kofar Gadon Kaya, a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano, Dr. Aliyu Yunus, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su daina shagaltuwa da jin daɗin duniya, su kuma riƙa tunawa da mutuwa da ranar komawa ga Allah.

Dr. Aliyu Yunus ya yi wannan kiran ne a cikin hudubar Juma’a mai taken “Alamomin Tashin Ƙiyama na ƙara bayyana, amma mutane na shagaltuwa da duniya”, inda ya bayyana cewa duk da irin abubuwan da ke faruwa a duniya da ke tunatar da mutum game da ƙarfin Allah da ƙarancin rayuwar duniya, mutane da dama na ci gaba da rayuwa cikin sakaci da mantuwa da Lahira.

Limamin ya ce ya kamata mutum ya fahimci cewa duniya ba wurin zama na har abada ba ce, don haka bai kamata son dukiya, matsayi, jin daɗi da sauran abubuwan duniya su shagaltar da shi daga yin ibada da tanadin abin da zai amfane shi bayan mutuwa ba.

Dr. Aliyu Yunus ya kuma ja hankalin jama’a kan yawaitar bala’o’i da manyan abubuwan ban tsoro da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa ya kamata su zama darasi da tunatarwa ga mutum, su sa shi ya ƙara komawa ga Allah tare da gyara rayuwarsa.

Ya kawo misalin girgizar ƙasa da ta faru a ƙasashe daban-daban a shekarar 2026, musamman a Colombia, inda wata girgizar ƙasa mai ƙarfin 7.4 ta afku a ranar 10 ga Agusta a yankin Chocó, lamarin da ya haddasa mummunar barna da asarar rayuka.

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya haura 300, yayin da dubban mutane suka jikkata.

Haka kuma Dr. Aliyu Yunus yace an samu manyan girgizar ƙasa a Venezuela, inda aka samu manyan girgizar ƙasa guda biyu a watan Yuni, yayin da Peru ta fuskanci girgizar ƙasa mai ƙarfin 7.2 a watan Agusta.

A nahiyar Asiya ma, Indonesia ta fuskanci wasu manyan girgizar ƙasa a shekarar 2026, ciki har da wata mai ƙarfin 7.4 a yankin North Maluku a ranar 1 ga Afrilu.

Sauran manyan girgizar ƙasa da aka samu a duniya a shekarar 2026 sun haɗa da girgizar ƙasa mai ƙarfin 7.5 a Tonga, 7.3 a Vanuatu, da 7.1 a yankin Sabah na Malaysia.

Dr. Aliyu Yunus ya bayyana cewa irin waɗannan abubuwan ya kamata su sa mutum ya tambayi kansa ko yana cikin shirin fuskantar ranar da ba za a samu damar komawa duniya domin gyara abin da aka aikata ba.

Ya ce mutuwa ba ta da shekaru, ba ta da lokacin da mutum ya tsara, kuma ba ta jira sai mutum ya kammala dukkan burinsa na duniya ba.

Limamin ya gargadi Musulmi da kada su bari son duniya ya mamaye zukatansu har su manta da Allah, yana mai jaddada muhimmancin yin salla, tuba, sada zumunta, taimakon mabukata da kuma aikata ayyukan alheri.

Ya kuma bayyana cewa abin da ya fi dacewa ga Musulmi shi ne ya yi amfani da lokacin da Allah Ya ba shi wajen gyara rayuwarsa, domin babu wanda ya san lokacin da ajalinsa zai zo.

Dr. Aliyu Yunus ya yi addu’ar Allah Ya shiryar da al’umma, Ya sa su kasance cikin masu tunawa da shi a kowane lokaci, Ya kare su daga bala’o’i, sannan Ya ba su ikon yin kyakkyawan shiri kafin ranar da kowa zai koma ga Mahaliccinsa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version