Rahotanni daga daga unguwar Zango a cikin birnin Kano na nuni dacewa,wani matashi ya rasa ransa bayan da aka zargi wasu Yan Daba da kasheshi ta hanyar caka masa wuka .

A yayinda yake zantawa da manen labarai wani mazaunin unguwar da ya nemi a boye sunansa yace ana zargin yan dabar da daukar fansa akan wani matashi da ake rade radin Shima dan dabar ne .

Tuni kowa ya kama gabansa aka shiga gida aka rufe kofa a unguwar ta Zango bayan jami’an tsaro sun fara harbin iska .

A hirasu da manema labarai Yan unguwar ta zango sun nemi Yan dabar da su daina fadansu a cikin jama’a ,maimakon hakan su rika tafiya wajen gari ko cikin Daji idan ya zama dole sai sunyi fadan daban .

TST Hausa ta rawaito cewa unguwnanin birnin Kano ya zama dandalin fadan Daba a yan kwanakin biyo bayan wasannin Premier league na kasa da aka buga a kano .

A bayan an gano cewa rikicin fada dabar ya samo asali ne bayan da wasu Yan Daba daga unguwar Fagge suka kuduri aniyar yin ramuwar gayya akan kisan Wani matashi da aka zargi Yan kofar mata dayi a wani lokaci da ya wuce ,Wanda sukayi amfani da wasan kano pillars da aka buga a birnin Kano aka tashi rikicin dabar daga bacci.

An buga wasan ne tsakanin Kano pillars da Katsina United a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata 

A ranar Talata ne Yan sandan Kano suka kama mutane biyu da ake zargi suna da hannu wajen kashe mutane biyu .

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version