Limamin masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake Unguwar Gadon Kaya a karamar hukumar Gwale a Kano Dr. Abdullah Gadon Kaya, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su guji zalunci a kowane fanni na rayuwa, yana mai gargadin cewa duk wanda ya tauye wa mutane hakkinsu, to babu shakka zai fuskanci hukuncin Allah, ko da kuwa ya kubuta daga hukuncin duniya.

A cikin hudubar da ya gabatar, malamin ya bayyana cewa daya daga cikin manyan matsalolin da suka dabaibaye al’umma a yau shi ne yadda mutane suka shagaltu da tara dukiya da neman abin duniya, har suka manta da lahira da ranar da za su tsaya gaban Ubangiji domin yin hisabi.

Dr. Abdullah Gadon Kaya ya ce zalunci ya yadu a cikin al’umma ta hanyoyi daban-daban.

Ya ce akwai masu zalunci a kasuwanni da ke cutar jama’a ta hanyar yaudara, rashin gaskiya da tauye hakkin masu saye.

Haka kuma akwai masu zalunci a gidajensu, inda suke muzgunawa iyalansu ko hana su hakkokinsu, yayin da wasu kuma ke zaluntar jama’a a wuraren aikinsu ta hanyar cin amanar aiki da amfani da mukami wajen tauye hakkin mutane.

Malamin ya kara da cewa abin takaici ne yadda ake samun mai iko yana danne wanda ke karkashinsa, yana mai cewa a Najeriya sau da yawa ana ganin na sama yana zaluntar na kasa, kuma da zarar mutum ya samu wata dama ko mukami, sai ya fara amfani da ikon da yake da shi wajen cutar da mutane maimakon yi musu adalci.

Ya kuma yi tsokaci kan shugabannin Najeriya, inda ya ce ya kamata su ji tsoron Allah tare da tuna cewa shugabanci amana ce, ba wata dama ba ce ta zaluntar talakawa ko tauye musu hakkokinsu.

Malamin ya ce adalci shi ne ginshikin shugabanci nagari, kuma zalunci ba ya haifar da dawwamammen ci gaba.

A karshen hudubar, Dr. Abdullah Gadon Kaya ya yi kira ga masu fuskantar zalunci da kada su yanke kauna, yana mai cewa Allah ba Ya barin hakkin wanda aka zalunta.

Ya ce:
“Duk wani azzalumi da ya dame ku a Najeriya, ku ba shi lokaci kawai.

A karshe ya ce Zalunci ba ya dawwama, ranar sakamako tana zuwa, kuma Allah Madaukakin Sarki shi ne Mafi Adalci kuma Mafi Iko wajen karbar hakkin wadanda aka zalunta.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version