’Yan bindiga sun kai hari garin Chiromawa da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu.

A yayin harin, ’yan bindigar sun kuma yi awon gaba da Sarkin Noma na Chiromawa, Alhaji Yusuf Nadabo.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Garun Malam, Alhaji Aminu Salisu Kadawa, ne ya tabbatar da lamarin yayin da yake zantawa da Arewa Updates.

A cewar Kadawa, maharan sun kai harin ne a garin Chiromawa, inda suka bude wuta kan al’umma, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu.

Ya ce bayan harin, ’yan bindigar sun tafi da Sarkin Noma, Alhaji Yusuf Nadabo, zuwa wani wurin da ba a bayyana ba.

Lamarin ya jefa mazauna garin Chiromawa cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da neman karin bayani kan halin da Sarkin Noman yake ciki da kuma matakan da hukumomin tsaro ke dauka domin kubutar da shi.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu wani karin bayani a hukumance kan inda aka tafi da shi ko ko an gabatar da bukatar kudin fansa ba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version