Gwamnatin Kano ta nemi hadin kan hukumomin gwamnatin tarayya domin yaki da shan miyagun kwayoyi a jihar da kewaye.
Daraktan kula da ayyuka na musamman AVM Ibrahim Umaru mai ritaya shine ya bukaci hakan.
A wata sanarwa da Daraktan AVM ya sanyawa hannu akan rabawa neman labarai yace neman hadin kan hukumomin gwamnatin tarayya masu yaki da shan miyagun kwayoyi ya zama wajibi domin magance matsalar shan miyagun kwayoyi a jihar Kano da ma makota.
Hukumomin da AVM Ibrahim yake neman hadin kansu a madadin gwamnatin Kano,sun hada da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC da hukuma tsaro ta farin kayan civil defense da sauransu.
Daraktan kula da ayyukan na musamman na gwamnatin Kano ya bayyana irin jajircewar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf keyi na magance yawaitar kayayyakin da ba su da inganci da kuma miyagun kwayoyi tsakanin al’uma.
Ya sanar da cewa, an samar da hanyoyin inganta rayuwar matasa da ci gaban rayuwarsu , tare da la’akari da hakan a matsayin muhimmin dabarun rage shaye-shayen miyagun kwayoyi da matsalolin zamantakewar jama’a
AVM mai ritaya ya jaddada irin rawar da tsarin nan na ayyukan yan sanda da jama’a ke takawa wajen samar da ingantaccen zaman lafiya a Kano ya na mai kira ga shugabannin al’umma, da iyaye, da cibiyoyi da su yi aiki tare domin a gudu tare a tsira tare.
Yace a karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, jihar Kano na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen ganin an gina al’umma.
A karshe AVM Ibrahim Umar yace taron ya zama kamar na wani mataki na farko da ake fatan ya kasance mai dorewa da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na gwamnatin tarayya da na jihohi,da ƙungiyoyin al’umma, da daidaikun mutane da suke sadaukarwa wajen magance abubuwan da zasu kawo cikas a zaman zamantakewar jama’a.
Gwamnatin Kano na neman hadin kan hukumomin gwamnatin tarayya dan yaki da shan miyagun kwayoyi
By tst2 Mins Read