Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa Sanatan Kano ta Kudu, Sanata Kawu Sumaila, ya fitar da ’yan yankinsa kunya ta hanyar ayyukan raya kasa da yake gudanarwa a mazabarsa.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin taron ƙungiyar Muryar Kano ta Kudu, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Coronation Hall a Kano.
Gwamnan ya jinjina wa Sanata Kawu Sumaila bisa irin ayyukan raya kasa da ya gabatar a Kano ta Kudu, inda aka nuna wa mahalarta taron ayyukan da Sanatan ya aiwatar.
Ya ce irin waɗannan ayyuka na nuna yadda wakilan jama’a za su iya amfani da damar da aka ba su wajen kawo ci gaba da sauƙaƙa rayuwar al’umma.
A nasa ɓangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma yabawa tare da gode wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a Kano ta Kudu.
Ya musamman ambaci gyaran madatsar ruwa ta Kafin Chiri da sauran ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a yankin, yana mai cewa waɗannan ayyuka za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar yankin.
Gwamnan ya kuma jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati da wakilan jama’a domin samun ƙarin ayyukan ci gaba da za su amfanar da al’ummar Kano.
