Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa wani mutum mai suna Prince Adeniyi Adeyemi Matthew na fuskantar zargin ƙirƙirar wata hukumar gwamnatin tarayya ta bogi tare da riƙa gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar (Director-General) na hukumar ba tare da wata shaida a hukumamce daga gwamnati ba.

A cikin bayanan da aka fitar, an ce wanda ake zargin ya yi amfani da takardun naɗin aiki da wasiƙu da hatimai da lambobin takardun gwamnati da ake zargin duk na bogi ne, domin ya yaudari jama’a da hukumomi cewa hukuma ce ta gaskiya ke gudanar da ayyukanta.

Rahotanni sun nuna cewa ya riƙa gudanar da ayyukansa daga wani ofishi da ke cikin sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja, inda yake karɓar baƙi daga cikin gida da ƙasashen waje tare da gabatar da kansa a matsayin babban jami’in gwamnatin tarayya.

Haka kuma, ana zarginsa da neman takardar Note Verbale daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, domin tallafa wa wasu da ya bayyana a matsayin ma’aikatan sabuwar hukumar wajen neman bizar Amurka.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce wannan lamari ya saɓa wa doka tare da barazana ga martabar gwamnatin tarayya da sahihancin takardun hukuma.

Saboda haka, ta buƙaci hukumomin tsaro da na shari’a su tabbatar an gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

A halin yanzu dai, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta gurfanar da Adeyemi a gaban kotu tare da wasu mutum biyu da har yanzu ake nema ruwa a jallo.

Ana tuhumarsu da haɗa baki, ƙirƙirar takardun bogi, damfara da kuma yin sojan gona ta hanyar kwaikwayon jami’an gwamnati.

Sai dai, kamar yadda doka ta tanada, waɗannan zarge-zarge ne kawai a halin yanzu, domin kotu ce za ta yanke hukuncin ko suna da laifi ko kuma ba su da laifi bayan kammala shari’ar.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version