Shelkwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana Jagoran yan bindigar nan Bello Turji, a matsayin tamkar wata gawa dake tafiya a doron kasa .

Shekwatar ta bayyana hakan ne biyo bayan barazanar da Turjin ya yi kan sojoji da al’ummomi a jihar Zamfara na cigaba da kai hare hare.

Rahotanni nacewa ,Turji ya hana jihohin Arewa maso yamma zama lafiya musamman,Zamfara Katsina  da Sokoto da sauransu.

Turji, a cikin wani faifan bidiyo , ya kalubalanci sojojin Najeriya, inda ya zarge su da kai wa tsofaffi hari tare da neman a sako wani abokinsa Baka Wurgi da ke tsare a hannusu.

Ya kuma yi barazanar kaddamar da hare hare akan al’ummar Zamfara a sabuwar shekarar 2025 matukar ba a biya masa bukatunsa ba.

Da yake mayar da martani yayin taron karshen shekara da aka yi a Abuja , Daraktan kula da ayyukan yada labarai na shelkwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya yi watsi da barazanar Turji a matsayin maganar banza, yana mai shan alwashin cewa ‘Bellon ya fara kidaya kwanakin barinsa duniya.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da farfagandar Jagoran yan ta’adda game da abin da ya faru a Sakkwato, yana mai cewa, Yan ta’adda suna ci gaba da yada farfaganda ne domin kawar da hankalin yan Najeriya.

Buba ya bayyana kwarin guiwa game da ayyukan sojoji a shekarar 2025, inda ya yi hasashen fatattakar ‘yan ta’adda a Najeriya gaba daya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version