An garzaya da mutane 24 ranga ranga zuwa asibiti a garin Bida na jihar Naija saboda wata bakuwar cuta data barke a garin.
A ranar Talata ne matasa da magidanta da matan aure suka mamaye wata motar tankar man girki data fadi suna ta kwasar man duk da yadda jami’an tsaro sukaita hanasu amma basu hanu ba.
Saidai rahotanni nacewa watakila barkewar bakuwar cutar bata da alaka ko nasaba da amfani da wannan man girki na tirelar data fadi,sakamakon yau mako daya kenan da billar bakuwar cutar.
Zuwa yanzu an sallami mutane 20 daga asibitin gwamnatin tarayya na Umaru Sanda Nyadako dake garin Bida a jihar ta Naija.
Bakuwar cutar ta bazu ne zuwa cikin garin saboda karancin hanyoyin sadarwa da za,a iya sanar da ma’aikatan lafiya na kusa.
Abdulmalik Umar wanda wani mazauni ne a garin Bida ya shaidawa jaridar Daily Truth cewa wannan matsala ta rutsa da yan uwansa guda biyu ,amma kuma an sallame su zuwa gida.
Rahotanni nacewa haka kawai sai aga mutane suna yanke jiki suna faduwa kasa.
Saidai dukannin wadanda aka garzaya dasu asibitin ,anyi musu gwaje gwajen zazzabin cizon sauro da na Tipod.
Barkewar bakuwar cutar ya shafi garurwa da suka hada da garin Bida,da Laruta, da Ekoko,da Tutijiba,da Banin, da kuma Edogifu.
Wata majiya ta shaida cewa ana fargabar cigaba da samun barkewar cutar ,kuma ta yadu zuwa mutane 50 zuwa wannan rana ta Alhamis.