Daga Salisu Isa Galadanci

Gwamnatin jihar Jigawa da likitoci yan asalin Najeriya mazauna Saudiyya sunyi aikin idanu ga mutane dubu 4 a jihar ta Jigawa kyauta.

Mai taimakawa gwamnan Jigawa kan harkokin ilimi a matakin farko Dr Hauwa Mustapha Dahiru, ce ta bayyana hakan a wajen bude aikin bada magani da gilasai kyauta da kuma tiyatar Idanu ga al’ummar jihar akalla mutane dubu 4 da suka hada maza da mata da yara.

Anyi aiki ne a babban asibitin Dutse.

Dr. Hauwa Babura tace bada maganin ga masu fama da lalurar idanu wata nasara ce wanda kuma hakan zai taimaka wajen rage yawan masu larurar.

Haka kuma tace gwamnatin jihar Jigawa ta dauki batun lafiya da muhimmanci kasancewar yana cikin kudororin gwamnatin jihar goma 12.

Anasa jawabin jami’in shirin duba lafiyar idanun na Najeriya Dr Yusuf Umar Cedi, yace sunyiwa mutane 500 tiyatar idanu da kuma raba gilasan yin karatu guda 1000 baya ga duba daruruwan marasa lafiya da kuma basu magani kyauta.

Anasa jawabin magajin rafin Ringim, kuma jagoran gidauniyar Horozon Alhaji Mustapha Bako, ya godewa gwamna bisa bada tallafin aikin na maganin Ido a jihar.

Suma wasu daga cikin wadanda suka amfana da wannan tallafin aikin idanu sun bayyana jin dadin su.

An kammala aikin a wannan rana ta Laraba 22 ga watan Janairun 2025.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version