Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na maganace matsalolin da yara ke fama dashi na tamowa da mata masu juna biyu da suke fama da wannan matsala.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da hakan ne a lokacin kaddamar da shirin kula da kananan yara masu mafa da yunwa ta tamowa da mata masu juna biyu kafin haihuwa da bayan sun haihu.
Ana sa ran mutane dubu 300 ne zasu amfana da wannan shiri da aka sa masa suna Shirin kula da lafiya na Abba .
Shirin Kashi na biyu wanda gwamna Yusuf ya kaddamar a asibiti Kula da marasa lafiya a matakin farko dake daura da shalkwatar karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, ya nuna damuwa kan halin da kananan yara ke ciki a Kano.
Shirin wanda ya hada da baiwa mata masu juna magani kyauta,da kula da lafiyarsu da kula da lafiyar kananan, gwamna yace zaici gaba da yin duk mai yiyuwa dan tabbatar da ingantuwar lafiyar yara da mata masu juna biyu a Kano.
Gwamnan ya shaida cewa za’a rabawa irin wadannan asibitici naurori masu kwakwalwa a mazabun Kano gaba daya ,dan taimakawa wajen daukar bayanai na marasa lafiya
Rahotanni nacewa ,a kwanakin baya ne gwamna Yusuf ya amince da yiwa asibitin kwaskwarima,wanda ya nuna gamsuwa da aikin da ya gani anyi
A watan Augusta da ya gabata ne gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da irin wannan shiri a karamin asibitin kula da marasa lafiya a matakin farko dake unguwa uku a karamar hukumar Tarauni .
Gwamna Yusuf da ga nan yaci alwashin daga likkafar asibitin na Kumbotso zuwa babban Asibitin kwanciya.
Anasa jawabin tunda farko kwamishinan Lafiya na kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ya nemi mata masu irin wadannan yara dake fama da tamowa su hanzarta kai yaransu asibitoci dan a kula dasu
Yace Shirin zai fadada zuwa mazabu da kananan hukumomin kano anan gaba