Ana sa ran kuɗin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027 zai ƙaru a ƙasashe da dama, yayin da jami’an da ke kula da harkokin Hajji suka bayyana cewa wannan ƙarin ba ya da alaƙa da wata ƙasa guda ɗaya, illa dai sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a duniya.

Bayanan da suka fito sun nuna cewa hauhawar farashin masauki, abinci, sufuri da sauran ayyukan da ake bayarwa a ƙasar Saudiyya, tare da ƙarin haraji da kuɗaɗen gudanarwa, na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙara tsadar aikin Hajji.

Haka kuma, tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ya jawo ƙarin kuɗin zirga-zirgar jiragen sama, yayin da sauyin darajar kuɗaɗen ƙasashe ke ƙara wa alhazai nauyi, musamman daga ƙasashen da kuɗinsu ya ragu ƙarfi idan aka kwatanta da dalar Amurka ko Riyal na Saudiyya.

Masana sun ce irin wannan yanayi ne ya haifar da tashin kuɗin Hajji a shekarun 2018 da 2020, inda kusan dukkan ƙasashen da ke tura mahajjata suka fuskanci ƙarin kuɗaɗen gudanar da aikin.

Sai dai, domin rage tasirin wannan ƙarin ga mahajjata, gwamnatoci da hukumomin kula da aikin Hajji na ƙasashe daban-daban suna nazarin hanyoyin rage kashe kuɗi.

Daya daga cikin matakan da ake dubawa shi ne amfani da jiragen saman da ke komawa ƙasashensu ba tare da fasinjoji ba bayan sauke mahajjata, domin su ɗauko masu yawon buɗe ido ko sauran matafiya zuwa waɗannan ƙasashe.

Ana sa ran wannan tsari zai taimaka wajen rage asarar da kamfanonin jiragen sama ke yi, wanda hakan na iya taimakawa wajen rage kuɗin tikitin jirgi da kuma sauƙaƙa wa mahajjata nauyin kuɗin Hajji a shekaru masu zuwa.

Duk da waɗannan ƙoƙarin, masana na ganin idan hauhawar farashi da sauyin tattalin arzikin duniya suka ci gaba, akwai yiwuwar kuɗin Hajji ya ƙara tashi a shekarar 2027 fiye da yadda aka saba.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version