Kwamishinan yada labarai na Jihar kano Kwamared Ibrahim Abdullahi wayya yace zuwan gwamna Abba Kabir Yusuf yasa Kano ta kubuta daga hannun masu watanda da dukiyar al’umma.

Kwamishinan yada labaran ya bayyana hakan ne a ranar lahadi lokacin da yake kaddamar da kwamitin yada ayyukan gwamna Abba Kabir Yusuf a kafar sadarwa ta Facebook, wanda yace gwamnatin kano maici karkashin Abba Kabir Yusuf gwamnati ce da ke kula da amanar Al’umma.

“Badon Abba Kabir Yusuf ne a kujerar gwamnatin jihar kano ba, da yanzu anyi watandar kano”,Inji kwamishinan.

Yace da yanzu wasu yan tsirari sunyi kashi mu raba da kaddarorin gwamnati.

Ibrahim wayya yace yanzu lokaci ne na tallata ayyukan da gwamna Abba Kabir Yusuf yake wa Al’umar kano a kowane fanni.

“Kamr yadda ake Kiran gwamna da sunan Abba gida gida, haka kowane aikinsa sai ya shiga gida gida na Jama’ar jahar kano”,acewar Wayya.

Kwamishinan yada labaran na kano ya kara da cewa, yana daga cikin abinda yasa gwamnatin Kano ta kaddamar yan TikTok a makonni biyu da suka wuce domin yada ayyukan gwamnatin jahar kano.

A lahadin nan kuma aka kaddamar da yan Facebook, sannan za a kaddamar da yan Instagram nan gaba don sanar da duniya irin ayyukan alheri da gwamna Abba Kabir Yusuf yake yiwa Jama’ar kano.

Daga nan Ibrahim wayya ya ja hankalin kwamitin yan facebook din da aka kaddamar karkashin jagorancin Abdurrahman Hamisu, wato ( project promotion & advocation)kan su jajirce a sami canji wajen yada manufar gwamna Abba Kabir da jagora Rabiu Musa Kwankwaso.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version