Daga Ibrahim A makama

A bisa umarnin Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa data Jigawa da Benue sun  fara aiwatar da dokar yiwa motoci rijistar inshora da ake kira  Third Party Motor Vehicle, daga ranar 1 ga Fabrairu, 2025.

Wannan aiki zai ci gaba da gudana, don haka rundunar ta nemi masu motoci da direbobi a Najeriya su tabbatar sun samu inshorar akan lokaci.

A yanzu haka aikin yayi nisa a jihohin Adamawa da Benue da Jigawa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya tana gargadin masu motoci da direbobi kan rashin bin wannan muhimmiyar doka.

Duk wanda bai bi ba zai fuskanci matakan tilasta wa, ciki har da tara da hukunci.

Wannan shiri yana da nufin tabbatar da cewa masu motoci sun bi ƙa’idojin inshora da aka gindaya domin kare kansu da kuma sauran masu amfani da hanya.

A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Dankombo Morris, ya umarci jami’ai da za su aiwatar da wannan doka da su kasance masu kwarewa, biyayya da adalci a ayyukansu.

Haka nan ya yi gargaɗi cewa ba za a yarda da kowace irin cin hanci ko rashin mutunci ga jama’a ba, kuma duk wanda aka samu da hakan zai fuskanci hukunci.

Ana kira ga jama’a da su bada haɗin kai ga ‘yan sanda, domin wannan shiri yana da fa’ida ga kowa.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version