Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ba da umarnin gudanar da Sallar Rokon Ruwa a fadin jihar, biyo bayan jinkirin saukar ruwan sama da ake fuskanta a wannan lokaci.
A cikin sanarwar da ya fitar, Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa Musulunci ya tanadi yin Sallar Rokon Ruwa (Salatul Istisqa’i) a duk lokacin da aka fuskanci ƙarancin ruwan sama ko fari, domin neman rahama da taimakon Allah Madaukakin Sarki.
Ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su tuba zuwa ga Allah, su yawaita istigfari, addu’o’i, kyautata mu’amala da juna tare da nisantar dukkan ayyukan da ke jawo fushin Ubangiji, yana mai jaddada cewa waɗannan su ne hanyoyin neman rahamar Allah da saukar da ruwan sama mai albarka.
Shugaban Majalisar Malaman ya kuma bukaci malamai, limamai, shugabannin al’umma da sauran Musulmi su fito domin halartar Sallar Rokon Ruwan a ranar, lokaci da wurin da aka tsara, tare da nuna ƙasƙantar da kai da cikakken tawakkali ga Allah.
Ya bayyana cewa Allah Shi kaɗai ne Mai iko da saukar da ruwan sama da yalwar arziki, don haka ya kamata kowa ya himmatu wajen addu’a domin Allah Ya saukar da ruwan sama mai albarka, Ya kawar da fari, Ya albarkaci gonaki, dabbobi da rayuwar al’ummar Kano baki ɗaya.
Ya shaidawa TST Hausa cewa za’a gudanar da Sallar ne ranar Lahadi 9 ga watan watan Agusta 2026 a Masallacin Juma’a na Dangi dake kan titin zuwa Zaria da karfe 9 na safe.
