Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kafa Majalisar Sulhunta Masu Fadan Daba domin nemo hanyoyin kawo karshen rikicin daba da ke addabar wasu sassan jihar.
Kwamared Waiya ya ce majalisar ta kunshi mutane 70, karkashin jagorancin Abdullahi Muhammad, inda za ta binciki musabbabin fadan daba da kuma hanyoyin da za a kawo karshen matsalar.
Ya bayyana cewa majalisar za ta binciki mutanen da rikicin ya rutsa da su, asarar rayuka da dukiyoyin da aka samu a baya, da kuma matasan da suka kudiri aniyar daukar fansa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar za ta yi aiki karkashin shirin tudun mun tsira na “Save Corridor”, wato wata hanya ta musamman da za ta bai wa matasan da ke son kubuta daga rikicin daba damar samun mafaka da tallafin da zai taimaka musu su fice daga harkar.
Ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnati na ceto matasa daga sake fadawa cikin rikicin daba, tare da samar musu da damar komawa cikin al’umma cikin kwanciyar hankali.
