Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta tabbatar da barkewar wani sabon nau’in cutar coronavirus a kasar China.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Ghebreyesus ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na gaggauwa a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Rahotanni nacewa Kwamitin gaggawa na WHO kan annoba da cututtuka ya gana da masu ruwa da tsaki dan gano yadda za’a dakile wannan cuta.
Tedros ya kuma gabatar da wasu shawarwarin da kwamitin gaggawar ya bayar don shawo kan barkewar cutar, da suka hada da hanzarta samar da alluran rigakafi da magunguna da kuma yaki da yada labaran karya.
Wannan shine karo na shida da WHO ke amfani da wannan Shirin mai taken “Gaggawar kula da Kiwon Lafiyar Jama’a na da mahimmaci”
Sama da shekara 15 aka kafa kwamatin a majalisar dinkin Duniya.
Shekaru biyar kenan da gano cutar Coronavirus ta farko a watan Disamba na shekarar 2019 a garin Wuhan na kasar China.
A wasu hotunan bidiyo da ke yawo a China anga yadda ake layi a asibitocin yankuna da dama domin duba al’uma da suke fama da mura domin domin gano ko wannan curar ta biyu nada alaka da ta shekarar 2019