Shugaban kasar Amurika Donald Trump ya tabbatarwa da Amurikawa cewa duk abinda zaisa a gaba a wa’adin mulkinsa na biyu kasarsa ta Amurika itace ta farko Kuma akan gaba.

Trump ya bayyana hakan ne bayan ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin Shugaban Kasar Amurika na 47 a wani biki da akayi a dakin taro na Capitol hill a birnin Washington DC.

An shirya taron a daki ne saboda tsananin sanyi da ake fama dashi a sassan Amurikan.

Trump yace zai budewa Amurika sabon shafi na Shugabanci.

Yace gwamnatin Amurika kafin zuwansa ta fuskanci kalubale da dama , musamman tsangwama, Amma yace dole ne yanzu a sauya tsari.

Yayi alkawarin daukar mataki mai tsauri akan duk yan kasashen waje da suke aikata laifuka saboda samun wajen zama a Amurika.

Yayi alkawarin cewa gwamnatinsa zata mayar da miliyoyin bakin haure zuwa kasashensu.

Trump ya kuma ce a shirye yake ya hidimtawa Amurikawa,tare da dawowa da Amurika martabarta.

Shugaban Amurikan yace yana sane da yadda wasu yan adawa suka so ganin bayansa da karbe masa yancinsa tun lokacin da yake yakin neman zabensa.

Ya godewa dukannin magoya bayansa da suka zabeshi a zaben da akayi na watan Nuwamban 2024.

Ya kuma shaida cewa zai farfado harkokin kasuwancin fitar da danyen Mai da Iskar Gas zuwa kasashen waje.

Daga nan yayi tsokaci akan rawar da gwamnatinsa zata taka akan sauyin yanayi da ake Cece kuce akansa a tsakanin kasashen duniya.

A jawabin nasa Trump yace zai kasance mai martaba zaman lafiya a duniya, shiyasa ya ce Amurika ta janye hannu daga duk wani yaki na kasahen duniya.

“Munfi kwarewa akan duk wani abu da ba zai yiyu ba;Inji Trump

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version