Wasu ‘yan siyasa a Kano sun fara kira ga tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya koma jam’iyyar PRP ta malam Aminu Kano domin kaucewa duk wani kalubalen siyasa.

Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai daga Ƙaramar Hukumar Dala a ƙarƙashin jam’iyyar PRP a Jihar Kano, Hon. Ali Rabiu Ali Daddy,wanda ya taba yin wannan kiran yace komawar kwankwanso PRP zai huce Haushi kuma ya dawo jam’iyyarsa ta gida.

Ali Daddy ya ce PRP ita ce jam’iyyar da aka assasa bisa manufofin adalci,da gaskiya da kare haƙƙin talakawa, yana mai cewa duk mai ikirarin bin tafarkin Malam Aminu Kano ya kamata ya kasance a cikin jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa idan Kwankwaso ba ya da niyyar komawa PRP, to ya kamata ya daina nuna fushi da ci gaba da sukar wasu jam’iyyun siyasa, tare da rungumar siyasar haƙuri, tattaunawa da mutunta ra’ayoyin sauran masu ruwa da tsaki.

A cewarsa, ƙofar PRP a buɗe take ga duk wani ɗan siyasa da ke son shiga, amma dole ne ya mutunta kundin tsarin jam’iyyar da shugabancinta ba tare da neman wata fifiko ta musamman ba.

Ali Rabiu Ali Daddy ya jaddada cewa siyasar Najeriya na buƙatar shugabanni masu haɗa kan al’umma da mutunta ƙa’idar dimokuraɗiyya, maimakon siyasar saɓani da rarrabuwar kawuna.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai fitar da wata sanarwa ko mayar da martani kan wannan kira da Ali Rabiu Ali Daddy ya yi ba.

TST Hausa ta rawaito cewa, kiran dan siyasar ya biyo bayan hukuncin kotun tarayya dake Lokoja a Kogi ta yi na soke rijistar NDC a matsayin jam’iyyar Siyasa a Najeriya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version