Gwamnan Jihar Kano,Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada cewa jar hula wata muhimmiyar alama ce ta tafarkin siyasar marigayi Aminu Kano, yana mai cewa gwamnatin sa ba ta da niyyar kawar da ita.
Gwamnan ya bayyana cewa jar hular tana wakiltar tarihi, akida da gwagwarmayar da Malam Aminu Kano ya yi wajen kare haƙƙin talakawa da tabbatar da adalci a cikin al’umma.
Ya shaida hakan ne a lokacin wata ganawa ta musamman da masu rike da mukaman siyasa a fadar gwamnatin Kano inda yace jar hula ba wata alama ce ta jam’iyya kawai ba, illa wata alama ce ta tarihi da ke tuna wa al’umma irin gudunmawar da Malam Aminu Kano ya bayar wajen ci gaban siyasa da wayar da kan jama’a.
“Jar hula dai ta Malam Aminu Kano ce, don haka ba za mu cire ta ba,” in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da girmama abubuwan tarihi da al’adun siyasar da suka taimaka wajen gina Kano da Najeriya baki ɗaya.
