Mai neman takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Gezawa da Gabasawa, Alhaji Rabi’u Yusuf Danmalam, ya yi kira ga magoya bayansa da al’ummar yankin da su kwantar da hankali, su rungumi ƙaddara, tare da ci gaba da bin doka da oda, yayin da ake jiran matakin gwamnati kan abin da zai biyo baya.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ya haɗa shi da masu ruwa da tsaki, shugabannin matasa, dattawa da wakilan mazaɓu daga ƙananan hukumomin Gezawa da Gabasawa.

A jawabinsa, Danmalam ya bayyana godiyarsa bisa irin goyon baya, addu’o’i da jajircewar da magoya bayansa suka nuna masa tun daga farkon tafiyar siyasa har zuwa wannan lokaci.

Ya ce duk da halin da ake ciki, lokaci ne na nuna haƙuri, hikima da biyayya ga shugabanni domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.

“Mun rungumi ƙaddara, kuma muna ƙara kira ga magoya bayanmu da su yi hakuri su jira umarnin gwamnati. Duk wani mataki da za a ɗauka dole ya kasance cikin lumana da bin doka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa siyasa hanya ce ta hidima ga jama’a da ci gaban al’umma, inda ya yi kira ga matasa da su guji duk wani abu da ka iya kawo tashin hankali ko barazana ga zaman lafiya a yankin.

A nasu jawaban, wasu daga cikin mahalarta taron sun jaddada goyon bayansu ga jagorancinsa, tare da bayyana aniyarsu ta ci gaba da bin shawararsa har sai an fitar da mataki na gaba daga hukumomi.

Sun kuma bayyana shi a matsayin jagora mai kishin al’umma, mai mutunta jama’a tare da fifita zaman lafiya a dukkan lamuransa.

Taron ya gudana cikin lumana da fahimtar juna, inda aka yi addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban mazaɓun Gezawa da Gabasawa baki ɗaya.

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version