Tsohon Sakataren gwamnatin kano Dr Abdullahi Baffa Bichi ya kaiwa tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ziyara.
Ziyarar tasa na zuwa ne bayan da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke Dr Abdullahi Baffa Bichi daga kurarsa a ranar Alhamis
Gwamna Abba ya sauke Dr Abdullahi Baffa Bichi ne shida Shugaban ma’aikata na Fadar gwamnatin kano Malam Shehu Wada sagagi shida kwamishinoni biyar,tare da sauyawa wasu wuraren aiki.
Babu wani labari da aka samu na takaimaimai akan abinda Sardauna Malam Ibrahim Shekarau da Dr Abdullahi Baffa Bichi suka tattauna akai.
Saidai wasu na ganin Dr Abdullahi Baffa Bichi din zai iya komawa gidan Shekarau yayinda wasu ke zargin zai iya komawa gidan Sanata Barau I Jibiril
Gwamna Abba Yusuf ya sauke Dr Abdullahi Baffa Bichi ne dan ya koma gida ya kula da lafiyarsa