Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ya rage karfin kashe kudi tare da jefa ‘yan Najeriya da dama cikin talauci a shekarar 2024.
Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na sabuwar shekara da aka yada kai tsaye a gidan rediyon jihar Oyo da sauran kafafen sada zumunta.
Yace babu wata maganar tsoro ko boye boye ,abinda Yan Najeriya a baya sukafi karfinsa yanzu yafi karfinsu.
Gwamnan, yayin da yake jawabi ga mazauna jihar, ya bayyana cewa Najeriya na fama da kalubalen tattalin arziki a tsawon shekarar da ta kare ta 2024.
Makinde, yayin da yake karin haske, ya ce gwamnatinsa za ta fito da hanyoyin magance tsadar rayuwa da talauci a wannan sabuwar shekarar ta 2025.
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta dauki kwararan matakai da za su kara karfin kashe kudi da kuma saukaka matsalolin tattalin arzikin da jama’ar jihar suke fuskanta a halin yanzu.
Ya kuma yi gargadin cewa za a dauki tsauraran matakan yaki da cin hanci da rashawa a jihar.
Yace bama iya Oyo ba kadai ,duk Kasar da cin hanci yayi katutu,to talauci da kaka nakayi sai ya jefa jama’a cikin kunci.