Kungiyar masana aikin Radiyo da Talabijin ta Najeriya SNB reshen Jihar Kano ta yabawa gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf abisa nadin da yayiwa Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya a matsayin kwamishinan yada labarai na Kano.

Kungiyar ta bayyana mukamin kwamishinan da aka baiwa Kwamared Wayya a matsayin abinda ya dace da cancanta.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun jami’ar tsare tsare da kuma sakatariyan kungiyar ta SNB ta Najeriya reshen Kano Aishatu Sule da Adamu Ibrahim Dabo.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Comrade Wayya ya yi fice wajen jajircewarsa wajen ganin ya sauke nauyin da duk yake wuyansa,sannan kuma an sanshi wajen kwazo a gwagwarmayar da ya shafe tsawon lokaci yanayi a kungiyoyin fararen hula a ciki da wajen Kano.

Ya bukaci masu aikin yada labarai, da masu buga labarai a yanar gizo gizo da sauran masu ruwa da tsaki a ma’aikatar yada labarai a jihar Kano da su baiwa sabon kwamishinan duk wani goyon baya da ake bukata.

Daga karshe kungiyar ta SNB ta taya Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 da haihuwa da kuma nasarorin da ya samu tare da yi masa fatan cigaba da sauke nauyin dake kansa a iya wa’adin mulkinsa a Kano

Share.
Leave A Reply Cancel Reply

Exit mobile version